BAN YI NADAMA BA!

®Jiddah Haulat Nguru (Mrs Bee)

(Gajeran labari don fadakarwa)

1⃣1⃣

Halliru ne ya hakurkurtar da ni kan zaman gidan.

"Idan kika bar gidannan yanzu ina za ki? Kin san dai ba za ki kama hanyar kauye alhalin ga Inna anan ba. Sannan asibitinsu ba a bukatar mai zaman jinya balle ki je can. A karshe kuma idan kika tafi kika bar aikinki a ina za ki samo kudin da za ki samawa Inna lafiya?."

Shiru na yi hawaye na zirara a idanuna. Tausayin kaina nake yi. Tabbas dukkanin abinda Halliru ya fada hakan ne.
" Ki yi hakuri watarana sai labari. Kwana nawa ne. Insha Allahu da izinin Allah ba za ki kara shekara biyu kina wannan bautar ba Hadiza. Ni kaina na matsu na ga na kammala komai anyi aurenmu. Yanayin rayuwar ne kawai ba dadi. Kina gani dai da kwalina na diploma na yi karatu. Amma aiki ya gagara. Tun mahaifina na nema, na zo nima ina nema dole ba yanda za mu yi haka muka hakura. Sana'a ma idan ba jari gareka ba ba ta yiwu ba. Da kyar na samu wannan aikin. Babu yanda zanyi haka na karba. Kina gani dai kudin bai fi wani ya kashe shi a wuni daya ba, shi nake a karba a wata, ga nauyi ya min yawa. Amma bana jin dadin yanda kike rayuwa a gidannan sam-sam Hadiza. Bana jin dadi. Amma ki kara hakuri watarana sai labari."

Shi ma idanunsa jajir yayi kamar zai yi kuka. Tabbas ni kaina ina tausayawa rayuwar Halliru. Shine babba a gidansu, duk wani nauyi a kansa yawanci ya ke. Lokaci zuwa lokaci haka za ka ga an zo nemansa daga gida, da na ga hakan kuwa nasan akwai matsala, ko babu na cefane ko kuma wani ba lafiya. Haka zai ta fama har ya ga ya biya bukatarsu. Fatana da rokona Allah ya shiga rayuwar Halliru ya taimaka masa, kamar yanda ya ke shiga tawa rayuwar ya ke taimakonta a kowanne lokaci.

Lokacin dana zo gidannan da aiki ko sallah ban iya ba cikakkiya, shi ya koya min. Ban iya karatun da ya wuce suratul fatiha ba, ita ma cike take da kura-kure, Halliru ya ke koya min Qur'ani har da na boko. Yanzu haka zan iya rubuta sunayen mutane da d'an gajeran sako. Su Hajiya ba ruwansu da addinina balle karatuna. Burinsu kawai na musu aiki. Ina gani Kulsum ita kadai har Malami ke biyota gida yana koya ma ta. A da dana ga ya zo da sauri zan je bayan filawoyi na labe dan nima ina koya. Da Kulsum ta fadawa momynta ta min fata-fata, ina ji ina gani na hakura. Ba dan Halliru ba, da bautar Allah ma ban san yanda zan yi ta ba.

Bayan kamar sati guda. Ban sani ba ashe Halliru ya samu Alhaji Kamilu ya fada masa matsala akan mahaifiyata. Yana rokonsa akan ya taimaka min. Nan ya ce masa ba matsala zai min maganar.

Halliru da murnarsa ya zo ya same ni yana fada min yanda suka yi da Alhaji. Nima na ji dadi sosai har da tsalle na. Dan Alhajin ya masa alkawarin har asibitin zai je ya ganota. Wai yana ta fada masa akan me ba mu sanar masa tuntuni ba.
Na ji dadin labarinnan sosai. Duk da a zuciyata ina mamaki sosai. Wai Alhaji ne yau yayi alkawarin zai taimaka mana. Mutumin da ko gaisuwata baya karba mai kyau, kallon arziki ma ban ishe shi ba a gidan. Ni a tunanina ma bai san da zamana ba a cikin gidansa. Dan kusan halinsu daya da matarsa. Bambancin kawai shi namiji ne, baya hantarata ko kyara. Amma takalmin kafarsa ya fini daraja a gunsa. Amma ni wannan ba shine damuwata ba  Kawai hango Innata nake ta samu lafiya kamar yanda ta ke da. Ina kwance akan cinyarta ina ta ba ta labari tana dariya.

Ranar haka na wuni da farin ciki sosai. Ko gajiya ba na yi da aiki. Allah-Allah nake na ji Alhaji ya dawo ya min maganar.

Tunda sassafe ranar asabar na ga Hajiya na ta shiri wai tafiya za su yi Abuja bikin 'yar abokin Alhaji ita da Kulsum. Nan na musu Allah ya kiyaye bayan anjajja min kunne akan 6arna da bata gida. Halliru ne ya dauke su zai kai su.

Ba dadewa da tafiyarsu Alhaji ya fito daga dakinsa, ni kuma a lokacin ina falo ina goge-goge. Ban ji fitowarsa ba sai kawai ganinsa nayi a zaune kan kujera daga shi sai gajeran wanda da singileti ya kura min idanu yana ta kallona. Gabana ya fadi ban san lokacin dana saki tsumman goge-gogen da ke hannuna ba ina fadin Innalillahi. Da sauri-sauri na yi hanyar kicin ba tare da na kara kallonsa ba. Muryarsa na ji a tsakiyar kaina ya na kirana. Cak na tsaya ba tare da na juyo ba. Gabana banda faduwa babu abinda ya ke. Ban taba ganin wani namiji a gabana da irin yanayin shigarnan ba, balle Alhaji babban mutum mai kamala.

"Zo."

Kawai ya ce. Ban san ta yanda zan iya juyawa na je gaban Alhaji ba. Dan kuwa ilahirin jikina banda kakkarwa babu abinda ya ke. Sunan Allah kawai nake ambata a zuciyata.
Da dan amo na ji yo muryarsa yana kara magana.
"Zo mana kina jina magana za mu yi."

Babu yanda na iya haka na juya kafafuna da kyar kamar wacce kwai ya fashewa a ciki. Kaina a kasa kamar wacce nayi wa sarki karya bana kara fatan kallonsa a cikin irin wannan shiga. A dan nesa da shi na tsugunna. Da kyar bakina ya iya furta "Ina kwana."

Muryarsa da fara'a sosai kamar ba shine wannan mutumin mai tsare gida da cin magani ba idan ana gaishe shi.
"Lafiya Hadiza ya jikin maman naki?"

"Da sauki." Na fada muryata kasa kasa.

Ya danyi gyaran murya. "Halliru ya fada min halin da mahaifiyarki ta ke ciki. Insha Allahu zan taimaka muku."

Ban san lokacin da murmushi ya kubce min ba. Sai dai har yanzu kaina a kasa ya ke na furta. "Nagode sosai Alhaji Allah ya kara girma da arziki."

"Amin ya rabbi. Yiwa kai ne ai."

Ya dan yi shiru na wani lokaci. Allah-Allah nake ya ce na tafi dan na gaji da zaman. Duk da naji dadin abinda ya fada amma sam zuciyata ban ji ta kwanta ba. Shirun na ji yayi yawa, a zatona ma ya koma dakinsa ne. Dan haka a hankali na dago kaina na dubi inda ya ke. Caraf idanuwanmu suka hade guri guda. Ashe tun dazun ni Alhaji ya kurawa idanu yana kallo, har da mayar da hannayensa bayan kansa ya tallafo.

A hankali na tashi da niyyar barin gurin. Na gaji da zaman. Sam zuciyata bata aminta da wannan kallon kurillan da Alhaji ya ke min ba.

Har na juya zan tafi na ji maganarsa.

"Ina za ki ban sallame ki ba. Ina son mu yi magana ne mai muhimmanci."

Kara tsugunnawa na yi a raina ina mamakin wacce magana ce Alhaji yau ya ke son yi da ni mai muhimmanci haka. Tunda nake rayuwa a gidannan banda ina kwana lafiya bata taba hadani da Alhaji ba. Amma yau ina ganin wasu sabbin al'amura daga gare shi. Ban kara mamaki ba sai da na ji ya kira sunana. Ban taba zaton yasan sunana haka ba sai yau.

"Hadiza ina son ki ban hankalinki sosai anan. Ki nutsu ki ji abinda zan fada miki. Ruwanki ne ki amince, hakan na nufin kin taimaki mahaifiyarki, ruwanki ne ki bijire hakan na nuni da cewa ba ki damu da rashin lafiyarta ba, sannan kuma barinki aiki a gidannan ya tabbata."

'Tabbas akwai matsala.' abinda na ji zuciyata ta fada min kenan bayan mummunat bugawar da na ji ta yi.